
A kalla mutane 11 ne wutar lantarki ta kashe har lahira, yayin da wasu da dama suka samu raunuka a Karamar Hukumar Zaria da ke Jihar Kaduna.
Hatsarin ya faru ne a ranar Laraba da rana a yankin Gwargwaje na karamar hukumar, inda ya jawo konewar gine-gine da guraren kasuwanci.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna ya bayyana cewa, hatsarin ya faru ne a dalilin tartsatsin babban layin wutar lantarki a kan karamin layin wutar lantarki, abin da ya jawo samun wutar da ta wuce ka’ida.
A jawabin da Shugaban Sashin Yada Labarai na Kamfanin, Abdulazeez Abdullahi ya fitar, ya nuna bacin ransa kan hatsarin tare da bayyana sakamakon farko kan binciken dalilin aukuwar hatsarin.
Wani mazaunin yankin da abin ya faru, Alhaji Bature Aliyu ya ce, wutar ta shafi dukkanin gidajen da ke yankin da barikin ‘yansanda, da kuma sabon bangare na Unguwar Major Aliyu da ma sabuwar unguwar Kauran Juli.