For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ya Tabbata Dole Masu Rike Da Mukaman Siyasa Su Sauka Kafin Su Tsaya Takara

Majalissar Dattawa a yau Laraba ta yi watsi da bukatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na gyara dokar zabe ta shekarar 2022.

Bukatar gyaran dokar dai ta sha kashi yau a majalissar, yayin da dattawan sukai watsi da ita a lokacin yin karatunta na biyu.

Kafin a zo ga batun yin ƙuri’a kan batun wanda kin amincewa da shi yai rinjaye, da yawan ‘yan majalissar sun yi maganganun nuna kin amincewa da kudirin goge sashin na 84(12).

Haka kuma ‘yan majalissar sun bukaci majalissar da ta yi biyayya ga umarnin kotu kan kudirin tare da yin watsi da shi.

Shugaban Kasa Buhari dai a makon da ya gabata ya nemi Majalissar Tarayya da ta sake gyara sabuwar dokar zaben da ya sakawa hannu ta hanyar goge sashi na 84(12) a cikin baka na dokar,  sashin da Shugaban ya baiyana da wanda ya saba da kundin tsarin mulki.

Sashin dai ya sanya cewar dukkanin masu rike da mukaman siyasa sai sun ajjiye mulkinsu kafin su tsaya takarar fidda gwani ko kuma su zama cikin masu gudanar da zaben fidda gwanin.

A dai Litinin din da ta gabata ne, Babbar Kotun Tarayya ta hana Shugaba Buhari, Babban Lauyan Kasa, da Shugaban Majalissar Dattawa yin gyarawa dokar.

To sai dai kuma a jiya Talata, Shugaban Majalissar Dattawan, Ahmad Lawan ya baiyana cewa babu wani hukuncin kotu da zai iya hana Majalissar Tarayya Gyara Dokar Zabe ta 2022.

Ya ce, hukuncin kotun ya sabawa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 kan rarraba karfin iko tsakanin bangaren zartarwa, majalissa da kuma bangaren shari’a.

Comments
Loading...