Sojoji sun sanar da karɓe iko a Nijar a hukumance, a inda wasu sojoji ƙalilan suka fito gidan talabijin na ƙasar suka tabbatar da juyin mulkin da suka yi.
Kakakin sojojin ƙasar Manjo Ahmadou Abdrahamane ne ya sanar da juyin mulkin inda ya sanar da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar, da kulle duka iyakokin ƙasar baki ɗaya.
Babu dai labarin halin da Mohamed Bazoum ke ciki ya zuwa yanzu, amma sojojin sun bayar da sanarwar sun tuɓe shi daga muƙaminsa.
Sun ce sun yi juyin mulkin ne saboda halin da Nijar ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziƙi, yayinda suka kuma sanar da dokar hana fita daga ƙarfe 10 dare zuwa 6 na safe a duk faɗin ƙasar.
Labari Mai Alaƙa: Mafi Yawan Shugabannin Najeriya Suna Da Ƙarancin Sanin Mene Ne Ci Gaba – Obasanjo
BBC Hausa ta rawaito cewa, Shugaban Ƙasar Benin, Patrice Talon wanda ke jagorantar tawagar ECOWAS na cikin ƙasar ya ziyarci Nijar ɗin, sai dai sun gaza cimma wata yarjejeniya da waɗanda suka tsare shugaban ƙasar bayan sun yi juyin mulkin.
Tun a safiyar jiya Laraba ne aka bayar da rahotannin kame gidan shugaban ƙasar tare da tsare Shugaba Bazoum a gidan, abin da ya janyo zanga-zanga daga magoya bayan Bazoum.
An sami rahoton cewa, sojojin sun yi harbe-harben jan kunne domin tarwatsa masu zanga-zangar.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya nuna rashin goyon bayan ƙasarsa da juyin mulkin.
Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya yi magana da Shugaba Bazoum kuma ya tabbatar masa da cewa yana da goyon bayan Majalisar.
Wannan ne juyin mulki na huɗu da aka yi a Nijar tun bayan samun ‘yancin kai da ta yi daga Faransa a 1960, kuma an ta yin yunƙurin junyin mulki da yawa a ƙasar da ba su yi nasara ba.
