For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yadda Kotu Ta Daure Matashi Kan Laifin Satar Kwanon Gyada

Daga Abdullahi Yawale

Babbar Kotun Shariar Musulunci mai lamba daya dake zamanta a Hadejia jihar Jihawa, ta daure wani matashi mai suna Musa Danladi dan shekaru 18 mazaunin unguwar Makara Huta Hadejia zaman gidan ajiya da gyaran hali na tsawon watanni biyu bisa aikata laifin satar kwanon gyada.

Alkalin kotun, Mai Sharia Yusuf Ibrahim Harbo, ya ce laifin da matashin ya aikata ya sabawa sashi na 180 da 144 na Kundin Shariar Musulunci na jihar Jigawa.

Kotun ta kuma bawa matashin horon aikin tsaftar muhalli a cikin al’umma, ko kuma matashin ya biya tarar ₦20,000.

Dan sanda mai gabatar da kara a kotun Sajent Abubakar Ubale yace ana tuhumar matashin ne da laifin satar kwanon gyada biyu wanda aka yiwa kimar kudi ₦2,000.

Kafin gurfanar da matashin a gaban kotun, binciken yan sanda ya gano ya saci tayar mota kirar Hilux ta kimanin naira ₦60,000.

Yanzu haka dai kotun ta dage sauraron tuhumar matashin kan zargin satar tayar motar zuwa ranar Litinin 27 ga watan Satumba, 2021.

Comments
Loading...