Rundunar yan sandan Najeriya a Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta kama wasu ƴan bindiga masu alaƙa da Bello Turji a wasu yankunan jihar.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, muƙaddashin babban sufeton ƴan sanda na yankin Sokoto da Kebbi da Zamfara DIG Ahmed Zaki Gwandu, ya ce dakarun ƴan sanda na musamman ne suka gano sansanonin da ke da alaƙa da Bello Turji.
An yi wannan samame ne a ƙarƙashin jagorancin rundunar Operation Sahara Storm a ƙananan hukumomi uku na Rabah da Goronyo da kuma Illela.
Zaki Gwandu ya bayyana cewa cikin wadanda aka kama ɗin har da wani babban mai samar wa su Bello Turji makamai mai suna Musa Mohammed Kamarawa mai shekara 33.
Karamawa ya amsa laifinsa a gaban ƴan sanda na cewa yana samar wa da ƴan bindiga makamai kuma a kwanan nan ma kafin a kama shi yake shirin aika wa Bello Turji wata mota maƙare da bindigogi na aƙalla naira miliyan 28.
Sannan akwai wani mutumin da ya ce shi shugaban wata rugar Fulani ne a yankin Dege da ke jihar Filato, kuma ya daɗe yana sayar da makamai ga ƴan bindigan. Sai dai ya yi rashin sa’a an kama shi a karo na farko da ya zo sayar da bindiga samfurin AK47.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Sokoto ta ce a jumulla an gabatar da mutum 57 ne a bainar jama’a, inda 37 daga cikinsu suka amsa laifinsu na kai hare-haren ƴan bindiga da kitsa munanan ayyuka da satar mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da mallakar muggan makamai da kuma kisan kai.
Kazalika, DIG Ahmed Zaki ya bayyana yawan abubuwan da jami’ai suka ƙwato a hannun mutanen da suka haɗa da harsasai 1,412 da ƙananan bindiga ƙirar pistol huɗu da kakin soji uku da ababen hawa huɗu da muggan ƙwayoyi da wayoyin hannu 16 da shanu 150 da sauran muggan makamai. Sauran sun ƙunshi layukan waya da gurnetin da ake harbawa da roka biyu da abin harba roka ɗaya.
BBC Hausa ta ji ta bakin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Sokoton, ASP Sanusi Abubakar, wanda ya ce an samu wannan nasara ce ta hanyar aikin haɗin gwiwa tsakanin sassan hukumar daban-daban.
“An turo yan sanda jajirtattu waɗanda AIG Ahmad Zaki Gwandu ya wakilta da sauran ma’aikatanmu a rukuni daban-daban da suka zo Sokoto saboda wannan matsala ta ta’addanci da ta yi ƙamari.
“Kuma a cikin kwana takwas akwai wurare da yawa waɗanda maɓoya ce ga yan bindiga. “An kai musu yaƙi har kusa da ƙofa kuma an samu nasara ƙwarai da gaske,” ya ƙara da cewa.
ASP Sanusi ya ce mutanen da aka kama suna da laifuka daban-daban da aka kamo su a waɗannan wurare maɓoya na ƴan ta’adda sun kai akalla 37.
An fattataki wasu a wurare kamar Dajin Gudun-Gudun da Rabbah da Isa da Bungo da Sangari da Dunawa Tsamaye da Tangaza da Heli da Goronyo da Mayel da Sakanau da Kuka da Zangon Isu.
Kan batun Musa Kamarawa da aka daɗe da sanin yana tafka ta’asa amma ba a kama shi ba kuwa, ASP Sanusi ya ce dama rundunar ta daɗe tana haƙonsa, kuma a yanzu ta yi nasarar kama shi, “da zarar bincike ya kammala to za a gurfanar da shi gaban kotu.
Ya kuma karyata zargin da ake yi cewa Musa Kamarawa na da uwa a bakin murhu, inda har zai sa a sake shi bayan kammala bincike.
Sannan ya ce a ƙoƙarin farautar Bello Turji ne ta sa aka kai ga kama wadannan na kusa da shi din, “saboda duk waɗannan da aka kama din wadanda suke tare da shi ne, kuma shi ma ana bibiyarsa da yardar Allah zai shigo hannu,” a cawarsa.
(BBC Hausa)