Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta ce Ministan Kwadago da Samar da Aiyukan Yi, Chris Ngige bai gaiyace ta zuwa wani zaman tattaunawa ba.
A dai ranar Laraba ne, bayan kammala zaman Majalissar Zartarwa ta Kasa, Chris Ngige ya ce, zai yi zaman tattaunawa da kungiyar a kokarin ci gaba da shawo kan matsalar yajin aikin da ta ki ci ta ki cinyewa wanda kungiyar ASUU ke yi.
Sai dai kuma daga baya, Shugaban Kungiyar ta ASUU, Emmanuel Osodeke ya ce, ba a sanar da kungiyar maganar wani zama da bangaren Gwamnatin Tarayya ba.
“Ba a gaiyace mu wani zama ba. Babu wani mambanmu da aka gaiyata. Muna da sakatariyarmu amma ba mu sami wata gaiyata ba daga bangarensu,” in ji shugaban ASUU a wata tattaunawa da gidan talabijin na CHANNELS a safiyar Alhamis.
“Matsalarmu da wannan gwamnatin, musamman da shi ministan kwadago ita ce, idan zaka fadawa duniya cewa ka sanya zaman tattaunawa wanda ma ba ka sa ba, ta yaya zakai tunanin mu yarda da sauran abubuwan da ka fada?
“Kamata yai ya tabbatarwa da duniya cewa, ya turawa ASUU takardar gaiyata zuwa zaman tattaunawa a ranar Alhamis.”
Farfesa Osodeke ya roki ministan kwadagon da ya fita daga batun sasantawa da kungiyar.
“Ya kamata ministan kwadago ya kyalemu mu ji da ministan ilimi. Shine ya kara lalata wannan al’amari har ya kai inda ya ke,” in ji shi.
“Shine ya yanke hukuncin wahalar da mu da yunwa a matsayin makaminsa, lokacin da ya ce in ba aiki ba biya.”
ASUU, wadda ta shiga yajin aikin da take ciki a yanzu tun ranar 14 ga watan Fabarairu, ta baiyana rashin cika alkawarin gwamnati kan yarjejjiniyarta da kungiyar.
Ngige dai a baya ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa, zasu daidaita da ‘yan kungiyar kwanannan, inda ya ce, Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf domin ganin an bude makarantun.