For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yajin Aikin ASUU: Gwamnatin Tarayya Ta Sanar Da Karin Albashi Na Kaso 23.5% Ga Malamai

Ministan Ilimi, Adamu Adamu, a ranar Talatar da ta gabata, ya sanar da cewa, gwamnati zata iya biyan karin albashin malaman manyan makarantu ne da kaso 23.5 cikin 100, yayin da su kuma farfesoshi zasu iya samun karin kaso 35 cikin 100.

Ministan ya kuma bayyana cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi gargadi kan sanya hannu a yarjejjeniyar da gwamnati ba zata iya cikawa ba.

Adamu Adamu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da shugabannin jami’o’i da sauran masu ruwa da tsaki a harkar jami’a.

Ya ce, “Gwamnatin Tarayya iya karin albashi na kaso 23.5% zata iya ga dukkan kalolin ma’aikatan Jami’o’in Gwamnatin Tarayya, sai dai masu matsayin farfesa wadanda zasu samu karin kaso 35%.

“Sannan kuma, kudaden alawuns na aiyuka masu tasowa a bangaren malamai da ma’aikata Hukumar Gudanarwar Jami’o’i zata na biya kan lokaci ga wadanda suka yi irin wadannan aiyukan.

“Haka kuma, za a samar da kudi Naira Biliyan 150 a kasafin kudi na shekarar 2023 a matsayin kudaden gyaran Jami’o’in Gwamnatin Tarayya, wanda za a baiwa jami’o’in a watanni ukun farko na shekarar, sannan kuma za a ware Naira Biliyan 50 a kasafin kudin 2023 domin biyan bashin alawunsa na karin aikin koyarwa (earned academic allowance) wanda shi ma za a biya a watanni ukun farko na shekarar.”

Comments
Loading...