Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya ba su da kwakkwaran dalilin ganin laifin Gwamnatin Tarayya kan yanda take tafiyar da lamarin yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).
Ministan ya bayyana hakan ne a tattaunawar da ya yi da CHANNELS TV a shirin POLITICS TODAY na Larabar nan.
Malaman jami’o’i dai sun fara yajin aiki ne tun a ranar 14 ga Fabarairu, 2022, to amma tun wannan lokaci ana tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da ASUU, sai dai kuma har yanzu, wannan tattaunawar ba ta haifar da da mai ido ba, abun da ke kara jawo cece-kuce a tsakankanin ‘yan Najeriya.
Lokacin da aka tambayeshi cewa, idan ‘yan Najeriya suka nuna rashin jin dadinsu game da yanda gwamnati ke magance da daddiyar matsalar, ministan ya ce, gwamnati ba ta da lefi.
“Idan ‘yan Najeriya suka ji ba dadi (game da gwamnati), ina tunanin ba su da kwakkwaran dalilin rashin jin dadin hakan game da gwamnati,” in ji shi.
“Me yasa zasu ji babu dadi? Fada min a naka ra’ayin, ta yaya abun ya zama lefin gwamnati ba lefin kungiyar ba?
“Zaka kalubalanci gwamnati ne kadai idan ta ki ta yi abun da ya kamata ta yi – bijiro musu da abun da take ganin zai biya musu bukatunsu. Babu wata bukata da gwamnati zata iya biyanta 100 bisa 100.
Ministan ya ce, Gwamnatin Tarayya ta gabatarwa da ASUU abun da zata iya a matsayin wani mataki na kawo karshen yajin aikin.
“Gwamnati ta riga ta gabatar da abun da zata iya. A matsayin minista, na san cewa abun da gwamnati ta gabatar shine mafi dacewa da abun da zata iya,” in ji shi. “Ba zaka yi sama abun da zaka iya ba.”