Wai shin har yanzu bamu yadda masifar da kasar nan ke ciki ba na ta’addanci, mummunan mulki, talauchi duk suna faruwa ne sakamakon rushewa da rashin ingancin ilimi bane? Tabbas kauda kayin da manyan kasar nan sukayi a kan wannan matsalar, ba karamin hatsari bane, kuma nau’e ne na rashin kishin kasa.
Ko muki ko muso ba dabara bace a wajen mutum akili yayi rayuwar kura tsira da na bakinki, kamar yadda zamantakewar Nijeriya take a yau, shugabannin da suka samu damar darewa bisa gadon mulki da yan kuntukurun su suke ganin su sun tsira musamman a harkar ilimi domin suna iya samawa yayansu ilimi ba kawai ta hanyar gwamnati ba.
Amma sun kasa fahimtar cewa bala’in barin al’umma da gurbataccen ilimi yana shafar kowa da kowa ne duk matsayin mutun kuma duk inda ya gudu yaje. Wai shin bala’in yan tadda, talaka kadai yake shafa? Ko wanda ya bar kauyen su ya tafi birni shi yana ganin ya tsira?
A wannan karon ma yar manuniya ta nuna Kungiyar ASUU zata shafe kusan kwana 90 suna yajin aiki, tunda sun gaza samun matsaya tsakanin su da Gwamnati. Dukka wannan ba shine abin mamakin ba, mabanbantan kalamu da ga jami’an gwamnatin dole ya bawa duk wani dan Nijeriya mamaki, ta yadda a waje guda a kaji cewa Babban Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya kafa kwamati da zai duba wannan takaddamar, wanda kwamatin zai shafe wata uku kafin ya kawo repotan sa, sai kuma gashi a wani bangaren Karamin Ministan Ilimi ya na cewa ai babu dalilin tsawaita yajin aikin da ASUU ke yi, saboda sun cimma matsaya tare da su. Wannan ba karamin tahin hankali bane ta yadda gwamnati daya tana baki biyu.
Duk dan Nijeriya mai kishin kasar sa, a yau ya yadda cewa ingancin ilimin primary da secondary school a fadin kasar nan a lalace yake, a yau duk wanda kaga ya kai yaran sa makarantun gwamnati to babu yadda ya iya ne, domin bashi da halin kai su makarantu masu zaman kansu.
Wannan ya sanya samun makarantu masu zaman kansu barkatai, wanda suma dewa daga cikin su basu da ingancin da ake bukata a wajen ilimantar wa. Rushewar makarnatun gwamnatin ya faru ne bisa tsawan lokacin da aka dauka na kawar musu kai daga mahukunta, haka suka ci gaba da tabarbarewa kamar yadda kowa ya shaida yanzu, kai wasu ajujuwan makarantun primary da secondary kasar nan dakin kiwon tumaki ma yafi su kyan gani, dakunan kwanan dalibai kuwa, dakin gidan yari ma yafi su nutsuwa.
Tofa! in har aka gi gaya wa gwamnati gaskiya, su kuma shugabnni suka kauda kai ga jamióin mu domin su ba dole bane sai ýayan su sunje ba, to nan da karamin lokaci duk manyan makaran tun Nijeriya zasu turmushe da dedecewa kamar yadda makaran tun primary da secondary gwmanati suka zama, domin wannan gwamnatin a yau bata bawa harkar ilimi muhimmmanci ba, sai dai ma kara gishiri take a kan ciwo ta wajen kirkiran sabbin makarantu don biyan bukatar kansu ta siyasa ba wai hangen makomar al’umma ba. A wani fuskar kuma ga dunbun private universities nan ana ta kirkira a kowane sako.
Ba sai nayi bayani ba akan yarjejeniyar tsakanin FGN (Gwamnatin Tarayya) da ASUU ba, tunda daga baya a irin wannan yana yin da ASUU ta shiga na yajin aiki, munga irin su shugaban cin Majalissar Dokoki ta kasa, Shugabannnin Addinai sun shiga tsakani, wanda a wancen lokacin har aka samu tsagaita wuta a kan wannan rikici, amma a yau kowa ya kauda kai a halin da ake ciki. Wai shin bama tunanin yaya Nijeriya zata shiga in har muka bari a kasa karasa ruguza ilimin manyan makaran tun mu?
Idan zamu iya tunawa ko watan November 2021, Shugaban Majalisar Wakilai ya jagoranci sasanto tsakanin wannan kungiya da gwamanti akan batutuwa guda hudu da suka hada da gyaran makarantu, biyan malamai bashin alawus din su, Manhajar biyan albashi ta UTAS maimakon IPPIS da kuma aiwatar da yarjejeniyar malaman da gwamnati.
Abin mamaki da takaici har yau ma fa wadannan sune bukatun ASUU, to wai me ne ne ya yi tarnaki ne na warware wannan matsalolin? Wai me ya saka ne gwamnatin ke jan kafa a kan wannan matsalolin?
Babu wani lokaci da wuce yanzu da manyan kasar nan za su shigo don ceto wannan makarantun , mu sani fa ba kawai jami’oi ba har sauran manyan makarantun kasar nan irin su Polytechnic da Colleges of Education suna cikin wannan matsaloli , kuma suma akwai irin wannan yarjejeniya tsakanin su da gwamanatin tarayya, domin ba abin mamaki bane suma in sun tsindima yaji aiki a kowane lokaci da ga yanzu.
A yau fa da ake kokarin shiga kakar zabe da kuma irin yanayin da kasar nan ke ciki, musamman irin tsananin talauchi tsakanin al’ummar wannan kasa ya zama dole a sanya tunanin miliyoyin matasan kasar nan da ke manyan makarantu, yaya makomar su ake so ta kasance? Shin wane tunani ake na ginar wannan kasar da wadannan matasan.
A yau kowa yasan a kwai dubban matasa a daji sun dauki bindiga suna ta áddan ci don neman kudi, wanda kowa yasan tasgaron da aka samu ne wajen bayar da ilimi mai kyau ya sanya su shiga wannan hatsarin da sunan hanyar samun rayuwa da kudi, har suka yanke kaunar samun ingantacciyar rayuwa cikin lumana a kasar su.
Wasu matasan kuma sun dauki keyboard da mouse suna tafka zamba ta yanar gizo, wanda suke ganin wannan ce kawai hanyar da za su sami rayuwa da kudi, rashin ingantacce da sahihi ilimi mai tarbiya ne ya kai wadannan matasan shiga wannan gararanbar, domin sun yanke kaunar cewa yanayin shugabancin kasar su ba zai basu damar cimma burinsu na rayuwa ba.
Kauda kan da manyan kasar nan keyi akan shawo kan gwamantin da al’umma suka zaba bisa muhimmin batu kamar ilimi ba zai haifar da ‘da mai ido ba, ya kamata a sa kishin kasa a ga an ceto rayuwar matasan mu kuma mu kaucewa rushewar makarantun mu da ma ingancin ilimin.
Ya zama dole kowa da kowa ya san cewa wannan matsalar ba kawai ta ASUU, Dalibai da Gwamnati bace, matsala ce ta kowa da kowa, ya zama dole manyan kasar nan su gaya wa gwamnati gaskiya don kawo karshen wannan matsalar.
Mu sani fa yayin da mu ka kaucewa ilimi to lahilci ne fa zai mana linzami.
Ahmed Ilallah
alhajilallah@gmail.com