Mutane 52 aka kashe a hare-hare daban-daban da aka kai kan wasu al’ummomi a jihohin Plateau da Niger.
Yayin da aka tabbatar da kisan mutane 18 bayan ‘yan bindiga sun kai hari kan kauyen Ncha da ke karamar hukumar Bassa a jihar Plateau.
Haka kuma an tabbatar da mutuwar mutane 34 a wasu kauyuka biyu na jihar Niger a jiya Laraba.
KU KARANTA: An Gano Gawarwakin Mutane Fiye Da 140 Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Zamfara
Harin na jihar Niger, ya yi kama da ramuwar gayya, inda a ‘yan makwannin da suka gabata ne wasu kwararrun ‘yan farauta da ‘yan sintiri suka kashe da dama daga ‘yan bindigar da ke addabar al’ummomin yankin.
‘Yan bindigar sun kai harin ranar Larabar ne a kan kauyukan Nakuna da Wurukuchi yayin da mutanen kauyukan suke gonakinsu suna girbe amfanin gonarsu.
Duk gidajen da ke kauyen Nakuna wadanda na mutane kimanin 200 ne an konesu a yayin da ‘yan bindigar suka kai harin suna neman ‘yan sintiri domin su yi ramuwar gayya.