‘Yan bindiga sun kai hari gidan Sarkin Hausawa na Anguwar Azara a Jere, kan titin Kaduna zuwa Abuja, inda sukai awon gaba da matansa tare da ‘ya’yansa mata guda hudu.
Da yake tabbatar da lamarin ga wakilin Daily Trust a tattaunawarsu ta wayar salula, Malam Ibrahim Tanko, ya baiyana sunayen matan nasa da Maimuna Ibrahim da Hauwa’u Ibrahim.
Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun saki babbar matar tasa, Hauwa’u, bayan sun gano cewa tana fama da ciwon hawan jini mai tsanani.
Malam Ibrahim Tanko ya kuma ce, ‘yan bindigar, wadanda suke dauke da muggan makamai, sun kai harin gidan nasa da misalin karfe 11:52 na daren Talatar jiya.
Ya kara da cewa, shi ya samu nasarar tserewa ta daya daga cikin kofofin gidan.
“Bayan sun duba ne, sun kasa samuna, sai suka tafi dakin da ‘ya’yana suke bacci, suka tilasta tafiya da su bayan sun nuna musu bindiga,” in ji shi.
Sarkin Hausawan ya baiyana sunayen ‘ya’yan nasa da Aisha Ibrahim, Farida Ibrahim, Zainab Ibrahim da kuma Hussaina Ibrahim.
Ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun kuma wuce zuwa gidan makotansa inda suka tafi mutane hudu, ciki har da mai shayarwa wadda aka baiyna sunanta da Laraba Umar.
“Sun baiyawa mijin matar matukar wahala har sai da ya fita daga haiyacinsa. Yanzu haka yana wani asibiti mai zaman kansa da ke Katari yana karbar magani,” in ji shi.
Sarkin Hausawan ya ce sojoji sun isa wajen da lamarin ya faru kimanin awa guda bayan ‘yan bindigar sun tafi da wadanda suka kama.
Lokacin da Daily Trust ta tuntubi mai magana da yawun ‘yansandar jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya baiyana cewa ‘yansandan ba su san da faruwar lamarin ba.
(Daily Trust)