Wadansu da ake zargi da cewa ‘yan ta’adda ne sun kai hari rukunin gidajen ma’aikatan Jami’ar Abuja a safiyar Talatar nan inda suka yi garkuwa da ma’aikata hudu na jami’ar tare da ‘ya’yansu.
Jami’ar ce ta sanar da hakan a shafinta na Facebook a safiyar Talatar nan.
Shugaban Sashin Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Jami’ar, Dr. Habib Yakoob, ya tabbatar da faruwar lamarin kamar yanda THE NATION ta rawaito.
Jami’ar ta ce, ana yin kokari domin tabbatar da an dawo da wadanda aka yi garkuwar da su.
Sakon Facebook din ya ce “wadansu da ake tunanin masu garkuwa da mutane ne sun farmaki rukunin gidajen ma’aikatan Jami’ar da safiyar yau.
“Ma’aikatanmu na samar da zaman lafiya, hadin guiwa da jami’an tsaro, sun bazama domin ganin an ceto wadanda aka kama din.
“Muna da rahoton da ke nuni da cewa ma’aikatanmu guda hudu da ‘ya’yansu sune wadanda wasu fararen hula sukai garkuwa da su.
“Ana yin duk mai yiwuwa domin ganin an samu kubuto da wadanda aka yi garkuwar da su. Tabbas wannan ranar bakin ciki ce a wajenmu.