‘Yan bindiga sun kashe sojoji 9,’ yan sandan MOPOL 3 da kuma jami’an hukumar tsaro ta Civil Defense (NSCDC) 3 yayin wani hari da aka kai kan sansanin sojoji a jihar Sokoto.
Majiyoyin tsaro da dama da suka bibiyi lamarin sun shaida wa manema labarai ranar Lahadi cewa lamarin ya faru ne a sansanin Burkusuma da ke karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakoto.
A cewar majiyoyin, ‘yan ta’addan sun isa sansanin sojoji da yawansu a ranar Juma’a inda suka fara harbi ba zato ba tsammani.
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Sabon Birni Idris Muhammad Gobir, wanda ya tabbatar da harin, ya ce har yanzu ba a ga jami’an tsaro da dama a sansanin sojojin ba.
“Mun samu rahoton harin daga wani mazaunin yankin ta amfani da hanyar sadarwa ta Nijar. Amma yanzu zan tuntube shi don karin bayani kan harin kuma in komo ga ku ‘yan jarida, “in ji Gobir.
Ya ce ‘yan bindigar sun kona motoci biyu na sintiri yayin harin.
Haka kuma, wani dan majalisar dokokin jihar Sokoto, Aminu AlMustapha Gobir, ya tabbatar da harin, ya kara da cewa jami’an tsaro 12 ne suka mutu nan take.
Wani kwamishina a jihar da ake kira da Garba Moyi ya tabbatar da harin inda ya kara da cewa ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Sanusi Abubakar bai amsa kira da tes da aka tura masa ba a lokacin hada rahoton.