Rahotanni daga jihar Sokoto a Najeriya na cewa ‘yan bidinga sun kashe akalla mutum 49 a wata kasuwa a garin Goronyo na jihar.
Wasu ganau sun tabbatar wa da BBC labarin inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da yamma, yayin da mutanen ke cin babbar kasuwar Goronyon.
Mutanen wadanda suka bukaci BBC ta sakaya sunayensu saboda tsaro sun ce ‘yan bindigar sun afka wa kasuwar ne a yayin da ta cika makil da masu hada-hada daga sassan jihar da ma wasu yankunan.
“’Yan fashin sun zo ne da misalin karfe 4:30 zuwa biyar na yamma suka zagaye kasuwar suka bude wuta ta kowane bangare,” in ji ganau din.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda a jihar, amma ba ta samu mai magana da yawun ‘yan sandan ba a kiran waya da ta yi ta yi masa.
Ya kara da cewa “Mutane duk suka rude wasu sun kwakkwanta a kasa don gudun harbin ya same su, yayin da wasu suka gudu amma masu tsautsayi sun rasa rayukansu.”
Ganau din sun ce an kidaya gawa 49 yayin da mutum 17 suka jikkata kuma tuni an kai su asibitin birnin Sokoto, “gawarwakin kuma an kai mutuwaren da ke babban asibitin garin Goronyo,” in ji daya ganau din.
Shaidun sun ce ‘yan sandan kwantar da tarzoma da ‘yan banga sun yi kokarin tarwatsa su amma ‘yan fashin sun fi su yawa don haka suka kasa shawo kan lamarin.
“Daga baya jami’an tsaro sun je amma lokacin ‘yan bindigar sun riga sun tafi,” in ji shaidun.
Kasuwar Goronyo na ci ne a ranar kowace Lahadi, kuma mutane na zuwa daga fadin jihar Sokoto da wasu jihohin har ma daga Jamhuriyyar Nijar.
BBC ta ce, ko a ranar 9 ga watan Oktoban da ake ciki ma akalla mutum 21 aka kashe a harin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Sabon Birni.
‘Yan bindigar sun bude wuta ne a lokacin da mutane ke cin kasuwar garin Unguwar lalle, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.