Hukumar ‘yan sandan jihar Imo da ke Arewa maso Kudancin Najeriya sun tabbatar da kisan da aka yiwa wasu sarakunan gargajiya guda 2 a jihar.
Al’amarin ya faru ne ranar Talatar nan a Nnenasa da ke Karamar Hukumar Njaba da ke jihar, inda mai magana da yawun ‘yan sandar jihar, Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Abattam, ya ce ‘yan sandan na cigaba da bincike kan kisan domin gano hakikanin abin ya faru yayin harin.
Sarakunan gargajiyar da aka kasha sune E. Duruebere na Okwudor da kuma Sampson Osunwa na Ihebinowerre wadanda duk aka kashe su a Njaba.
An rawaito cewa, ‘yan bindigar sun afkawa taron tattaunawar da sarakunan gargajiya ke yi tare da masu ruwa da tsaki a Nnenasa a ranar Talata, inda suka budewa sarakunan wuta tare da kasha sarakuna 2 nan take.
Harbe-harben sun sanya masu taron rikicewa tare da bajewa in ji majiyar da ba ta so a bayyanata ba saboda tsaro.
Majiyar ta kuma sanar da cewa mutane da dama sun jikkata yayin harin.
Har kawo yanzu babu wadanda suka dauki alhakin harin.
Ana daukar jihar Imo a matsayin cibiyar masu goyon bayan kafa kasar Biafra.