For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji A Kebbi

Gwamnatin Jihar Kebbi ta baiyana cewa wasu sojoji sun rasa rayukansu dalilin artabu tsakaninsu da ‘yan bindiga a Masarautar Zuru ta Jihar Kebbi.

Kisan sojojin ya zo ne kwana daya bayan an kashe wasu ‘yan sintiri 63 a Masarautar ta Zuru.

Gwamnan Jihar Abubakar Atiku Bagudu ne ya baiyana kisan sojojin a yau Laraba lokacin da ya karbi bakuncin Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Geoffrey Onyeama, a Birnin Kebbi.

Duk da dai Gwamnan, wanda ya sami wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Umar
Babale Yauri, bai baiyana adadin sojojin da suka ran nasu ba, ya kara da cewa, gwamnatinsa na yin iya bakin kokarinta wajen kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar.

Ya ce, “Tabbas kwanaki uku da suka gabata mun rasa ‘yan sintiri 65. Kuma a jiya ma mun rasa sojojin da suke fada da su.

A jawabinsa, Ministan Harakokin Kasashen Waje, ya baiyana cewa ya zo jihar ne domin ya jajantawa ‘yan jihar bisa kisan ‘yan sintiri 65 da akai.

Ministan ya kara da cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya umarce da kawo ziyarar a madadin gwamnati.

Ya kuma yi kira ga jihar da ta cigaba da tsayuwa wajen kokarin kawo karshen ‘yan bindigar da suka addabi jihar.

Comments
Loading...