Rundunar ‘yan-sandan jihar Jigawa ta ce, wasu ‘yan-bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe ‘yan-sanda biyu tare da yin garkuwa da mutum daya a karamar hukumar Taura.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan-sandar jihar, ASP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa faruwar lamarin a Dutse ranar Litinin.
Shiisu ya ce lamarin ya faru ne bayan da ‘yan-bindigar suka kai farmaki gidan wani Alhaji Ma’aru Abubakar da ke garin Kwalam sukayi awon gaba da shi.
“A jiya Lahadi ne 23 ga wannan wata, muka samu kiran gaggawa mai ta da hankali, cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari garin Kwalam da ke karamar hukumar Taura.”
Acewar kakakin rundunar ‘yan-sandan jihar, bayan samun rahoton, sun ta da tawagar ‘yan-sanda domin kai dauki wurin da lamarin ya faru, amma sun samu ‘yan bindigar sun gudu.
Yan bindigar sun harbe ‘yan-sanda biyu da suka hada da ASP Anas Usaini da Sunusi Alhassan a kusa da wata motar sintiri da ‘yan-bindigar suka kona kurmus.
“Bincike ya nuna cewa ‘yan-bindigar sun kai farmaki gidan Alhaji Ma’aru Abubakar mai shekaru 60 a garin Kwalam inda suka yi awon gaba da shi,” in ji Shiisu.
Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da wanda abin ya shafa, tare da cafke wadanda ake zargi.