For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Ɗan Majalisa A Kano

Wasu ‘yan bindiga sun sace mahaifiyar Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Jihar Kano, Isiyaku Ali Danja da tsakar daren da ya gabata.

Maharan sun shiga gidan Hajiya Zainab da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa da misalin ƙarfe 1:00 na dare ɗauke da makamai, inda suka tilasta wa mutan gidan cewa sai an kai su ɗakinta.

KU KARANTA: An Gano Gawarwakin Mutane Fiye Da 140 Da ‘Yan Ta’adda Suka Kashe A Zamfara

Saminu Danja wanda ɗa ne ga ɗan majalisar, ya faɗa wa BBC cewa ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton ɓarayin ba su tuntuɓe su ba.

Honorabul Isiyaku Ali Ɗanja, shi ne tsohon Kakakin Majalisar Kano kuma wakilin Gezawa a majalisar.

Yankin Arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da fuskantar sace-sacen mutane don neman kuɗin fansa, sai dai lamarin bai yi ƙamari a Kano ba kamar jihohi maƙotanta.

Daga: BBC Hausa

Comments
Loading...