For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Tsohon Mataimakin Gwamna

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye-Wado a garinsu na Gwagi da ke yankin Karamar Hukumar Wamba da sanyin safiyar yau Juma’a.

Wata majiya daga iyalan wanda tsohon Mataimakin Gwamnan ta tabbatar da faruwar al’amarin, inda ta bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun haura gidan ne ta kan katanga, inda suka shiga gidan ta tagar dakin matar gidan inda suka tafi da shi zuwa wajen da ba a sani ba.

Farfesa Onje Gye-Wado, wanda ya zama Mataimakin Gwamnan Nasarawa a tsakanin 1999 zuwa 2003, ya sha tsallake fadawa hannun masu garkuwa da mutane lokuta da dama kafin yau.

Da yake tabbatar da yin garkuwar, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yansandan Nasarawa, DSP Ramhan Nansel ya ce, ‘yansanda na yin iya bakin kokari wajen ganin sun kubutar da tsohon Mataimakin Gwamnan.

Ya kuma bukaci al’umma da su bayar da ta su gudunmawar ga rundunar ‘yansandan wajen ganin cewa an samu nasarar kubutar da wanda akai garkuwa da shin cikin gaggawa.

Comments
Loading...