Mukaddashin Babban Kwamandan Runduna ta 7, Brig.-Gen. Abdulwahab Eyitayo, ya ce sama da ‘yan ta’addan Boko Haram 8,000 ne ya zuwa yanzu suka mika wuya ga sojoji.
Ya ce ‘yan ta’addan sun mika wuya daga maboyarsu da ke dajin Sambisa, da kuma sauran maboyarsu.
Eyitayo, wanda kuma shi ne Kwamandan Sashi na 1na ‘Operation Hadin Kai’, ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu da tawagar masu yada labarai kan tsaro daga Abuja suka kai Maiduguri a Talatar nan.
Ya ce mika wuyan da ‘yan ta’addan da suka tuba suka yi, wani abin farin ciki ne, inda ya kara da cewa, kokarin sojojin ne ya haddasa wannan nasarar.
A cewarsa, daya daga cikin dalilan da ke sa su mika wuya cikin rikicewa shi ne karfin bude wuta da sojojin ke nunawa.
“Saboda dagiyar kowane mutum na da alaka da zaman lafiyar iyalinsa, wannan shine dalilin da yasa duk suke fitowa tare da iyalansu. Mun fara ganin alamun za su yi haka tun daga watan Yuni.
“Hareharenmu masu tsauri sun toshe hanyoyin samun abincin su da sauran kayayyaki, da boma -bomai, wannan shine dalilin da yasa suka fara mika wuya bayan haka kuma jinyoyi sun kama da yawansu.
“Hakan ya fi musu kyau, saboda a karshe sojojin za su share dukkan su da masu tausaya musu gaba ɗaya,” in ji shi.
Kwamandan ya yi gargadin cewa lokaci zai zo da ba za a sake samun kofar mika wuya ba, yana mai kira ga masu tausayawa ‘yan ta’adda da su bas u shawarar fitowa tare da mika wuya kafin lokaci ya kure.
Ya kara da cewa duk wanda ya goyi bayan makiyan zaman lafiyar jihar shima sojojin jihar za su dauke shi a matsayin makiyi.
Ya ce a yanzu sojojin sun jajirce fiye da kowane lokaci don tunkarar ‘yan ta’addan da magoya bayan su.
Dangane da yadda ake kula da ‘yan ta’addan da suka mika wuya, Eyitayo ya bayyana cewa sojojin Najeriya ne ke da alhakin karba, da tantance’ yan ta’addan.
Kwamandan ya bayyana cewa bayan haka, za a mika su ga gwamnatin Borno don ci gaba da daukar mataki.
Ya yi bayanin cewa adadin mai yawa na wadanda suka mika wuya, ya hada da mata da ‘ya’yan’ yan ta’addan, da kuma wadanda aka tilasta su shiga cikin ta’addancin.
Tun da farko, daraktan, hulda da jama’a na rundunar, ya ce rangadin kafafen yada labarai wani bangare ne na kokarin dakile labaran da ba daidai ba da na kawo firgici.
Nwachukwu ya yaba da kokarin da sojojin ke yi wajen matsa lamba kan ‘yan ta’addan.
(NAN)