For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Boko Haram Sun Kona Rumbunan Hatsi Da Gidaje A Borno

Mayakan Boko Haram sun kai hari kan kauyen Jibwiwi a karamar hukumar Hawul da ke Jihar Borno, inda suka kona gidaje da dama tare da kona rumbunan hatsi.

Rahoton da BBC Hausa ta samu sun cewa, an kona a kalla gidaje takwas da rumbunan hatsi da ya kunshi dawa da masara da sauran nau’ukan hatsi da dama.

’Yan Boko Haram din sun je kauyen ne a kan babura da yammacin ranar Litinin, haka kuma sun kona rumbunan ba tare da daukar komai ba daga cikinsu ba.

Wani dan kungiyar sintiri a kauyen ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, bayan mayakan sun kona gidaje da rumbuna a kauyen, sai suka wuce zuwa garin Ngulde da ke karamar hukumar Askira Uba, inda ‘yan sintirin suka samu nasarar murkushe su da taimakon mafarautan yankin.

Comments
Loading...