Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne an rawaito cewa sun yanka a kalla mutane 15 a wani shiryayyen hari da suka kai kan kauyuka biyu a Karamar Hukumar Jere da ke Jihar Borno.
A wani rahoto da jaridar DAILY TRUST ta wallafa, ‘yan ta’addar sun shiga kauyen Kofa da tsakar dare inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi abin da ya kai har zuwa safiyar Juma’a.
An kuma rawaito cewa, ‘yan ta’addar sun kuma kai hari kan kauyukan Molai Kura da Molai Gana inda suka yanka mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
Yanayin dai ya jefa mafi yawan mazauna kauyukan tserewa daga gidajensu inda suka gudu daji domin buya.
Wani babban mamba a kungiyar ‘yan kato da gora, Bukar Ali Musty, ya fadawa DAILY TRUST cewa, manoma suna noma a gonakinsu a kusa da Molai a gefen Maiduguri a ranar Alhamis lokacin da maharan suka yanka su.
Ya ce, a kalla gawarwaki 15 aka samu a safiyar Juma’a, wadanda bakwai daga cikinsu manoma ne da aka yanka su lokacin suna gona, sannan kuma maharan suka yanka mutane takwas da ba su ji ba ba su gani ba a cikin gidajensu.