‘Yan kungiyar Islamic State of West African Province, ISWAP, sun yi garkuwa da wani da ake kira da Bulama Geidem wanda yake aiki da General Hospital, Gubio da ke Jihar Borno.
Gwamnatin Jihar Borno ta bakin Kwamishinan Iliminta, Juliana Bitruce ce ta tabbatar da faruwar da hakan a yau Laraba.
“Da misalin karfe 2 na dare ne na Laraba, ‘yan ta’addar ISWAP suka kai hari garin Gubio, inda suka saci kayan abinci da man fetur daga motar bayar da agaji.
Da take baiyana lamarin a matsayin abin kaico, ta ce ma’aikacin lafiyar da akai garkuwa da shi yana daya daga cikin wadanda suka tsaya a wajen aikinsu duk da matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin.
“Ma’aikatar lafiyar za ta rubutawa jami’an tsaron da suka dace abun da ya faru, ciki har da Theatre Command, Operation Hadin Kai,” in ji ta.
Kwamishinar ta kuma yi fatan samun sakin ma’aikacin lafiyar cikin koshin lafiya.
NAN