Daga: Haruna Ahmad Bultuwa
Majalisar Wakilai ta bayyana cewa za ta sake gabatar da kudirin gyaran dokar zabe a ranar Laraba mai zuwa.
Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila ya ce, majalisar ta yanke shawarar sake yin aiki da kudirin tare da aikewa ga shugaban kasa cikin gaggawa domin ya amince.
Femi Gbajabiamila ya sanar da hakan ne a lokacin da yake jawabi ga mambobin Majalisar bayan dawowa daga hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.
KU KARANTA: Gwamnonin PDP Sun Zargi Jam’iyyar APC Da Ruguza Tattalin Arzikin Najeriya
Ya ce an gabatar da zabin fidda gwani na kai tsaye a cikin kudirin domin share fagen baiwa ‘ya‘yan jam’iyya damar shiga a dama da su wajen fidda ‘yan takara.
Shugaban Majalisar ya kuma sanar da fara gyaran Kundin Tsarin Mulki na Shekarar 1999 da Majalisar ke aiki a kai, za a tura zuwa majalisun jihohi domin gudanar da aiki tare kafin karshen watan Fabrairu, na shekarar 2022.