For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Majalissar Wakilai Sun Yi Watsi Da Bukatar Kara Kudin JAMB

Kwamitin Kudi na Majalissar Wakilai a jiya, ya yi watsi da bukatar Hukumar Shirya Jarabawar Share Fagen Shiga Jami’a, JAMB na kara kudin jarabawar.

Rijistaran Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, wanda ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba ya ce, saboda yanayin abubuwan da ke faruwa na tattalin arziki, ya kamata a kyale Hukumar ta dawo da tsohon farashin JAMB na N5,000 maimakon N3,500 da ake siyarwa a yanzu.

To amma, mataimakin shugaban kwamitin, Sa’idu Musa Abdullahi ya ce, mayar da tsohon farashi na N5,000 zai sanya matsatsi ga masu neman shiga makarantu da kuma iyayensu ko masu kula da su.

Oloyede, ya ce, “Mun gamsu da a ciremu daga cikin kasafin kudi, amma akwai sharuda. Daya daga cikin sharudan shine, misali, lokacin da dalibai sukai rijista a shekarar 2016, mun karbi N5,000 (a kowanne form), kuma haka aka dinga yi a shekaru 5 na bayan (wannan shekara) kafin na shigo JAMB. Lokacin da muka zo, mun sawa gwamnatin naira biliyan 7.5. Mun ji cewa hakan kamar ya yi yawa, sai muka nemi gwamnati da ta rage kudin jarabawar. Amma tun daga nan ba mu kara ko sisin kwabo ba.

“Ina ganin ya kamata mu mayar da shi N5,000 kamar da. Duba da hauhawar farashi, idan ma mun caji N10,000, ina dai bayar da misali ne kawai, babu wanda zai tambayi gwamnati ko kobo. Ban san wani waje a duniya ba, in banda Finland, da ke cajin mafi karanci kamar yanda JAMB take caji. A Finland mun san cewa komai kyauta ne.”

Comments
Loading...