Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa, (The National Primary Healthcare Development Agency, NPHCDA) ta tabbatar da cewa mutane 395 ne suka kamu da nau’in cutar polio da ake kira da Circulating Mutant Poliovirus Type 2 (cMPV2) a jihohi 27 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Daraktan Hukumar NPHCDA, Dr Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis, inda ya ce yaduwar cutar na da alaka da samun raunin garkuwa a jikin kananan yara.
KU KARANTA: Kaso 4.2 Cikin 100 Kawai Aka Gama Yiwa Rigakafin Korona A Najeriya
Ya alakanta hauhawar kamuwa da cutar da karancin bayar da rigakafin cutar wanda ya samo asali daga bugun da annobar Korona tai.
Dr. Faisal, ya kuma ce, samfurin cutar polio da ke yaduwar ta Polio-Virus Type 2 da akan samu a jihohi 27 da Anuja, ta saba da cutar polio wadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta baiwa Najeriya shaidar cewa Najeriyar ta fita daga jerin kasashe masu cutar da 2020.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa, Hukumar NPHCDA, za tai duk mai yiwuwa wajen ganin cewa an habbaka bayar da rigakafin cutar, musamman a jihohin da abun ya faru, domin a kare yaduwar cutar.