For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Najeriya Ba Sa Bukatar Magajinka Daga Bakinka – PDP Ga Buhari

Jam’iyyar People’s Democratic Party, PDP ta ce ‘yan Najeriya za su bijirewa duk wani dan takara da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress, APC za su gabatar a zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

Wannan na zuwa ne a takardar da aka saki ranar Alhamis wadda Sakataren Yada Labarai na Kasa na jam’iyyar, Debo Ologunagba ya sanyawa hannu mai taken ‘Kawai ka Tafi, ‘Yan Najeriya ba sa Bukatar Magaji daga Gareka – PDP ga Buhari.’

Jam’iyyar PDP ta kuma zargi shugaban kasa da gabatar da alkaluman bogi da ikirari marar tushe kan kokarinsa a hirarsa ta gidan Talabijin na Channels a ranar Larabar da ta gabata.

KU KARANTA: Ina Sane Da Irin Wahalar Da ‘Yan Najeriya Ke Ciki – Buhari

Jam’iyyar adawar ta ce alkaluman karyar da shugaban ya bayar, sun kara tabbatar da gaskiyar cewa, babu wani a cikin jam’iyyar APC da ba ya karya.

“A shirbicinsa na kokarin gyara matsalolinsa a office, Shugaba Buhari ya bayyana cewa, a karkashin mulkin PDP, tsakanin 1999 da 2014, an siyar da man fetur a kusan dala 100 kowacce ganga, amma a lokacinsa da jam’iyyarsa sai da ya fado dala 37 kowacce ganga.

“Irin wadannan kage ya saba da abun da ya dace da gaskiyar abin da aka sani, wanda shi shugaban ya sani cewa, lokacin da PDP ta karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu na 1999, ana siyar da gangar danyen mai dala 16.27 sannan kuma dala 80.42 da kuma dala 63.28 a watan Nuwamba da Disamba na shekarar 2014.

KU KARANTA: Wasu ‘Yan APC Na Neman Ficewa Sakamakon Matsalolin Da Suka Biyo Bayan Zabukan Shugabanin Jam’iyyar

“A lokacin Shugaban Kasa Buhari da APC, mai bai taba fadowa kasa da dala 16 ba kamar yanda aka samu a lokacin PDP, amma ya fara a dala 37 zuwa 39.44 kowacce ganga a shekarar 2016 sannan ya cigaba da kasancewa tsakanin dala 60 da dala 70 kowacce ganga kawo wannan lokaci da muke ciki,” in ji sanarwar.

Jam’iyyar ta kuma yi ikirarin cewa duk da rashin wadatar kudin mai a lokacin da ta karbi mulki, ta samu nasarar habbaka tattalin arzikin kasa, ta biya bashin da ake bin Najeriya, ta habbaka bangarorin samar da arziki, ta samar da yanayin kasuwanci mai dadi wanda ya jawo sanya hannun jari daga kasashen waje, sannan ta mik mulki ga Buhari da APC, Najeriya tana da karfin tattalin arziki na dala biliyan 550, kuma mafi karfi a Afrika sannan mai matsayi na 26 a duniya a shekarar 2015.

PDP ta ce Shugaban Kasa bai da amsar cewa, lokacin da gidan Talabijin na Channels gabatar masa da gaskiyar cewa, lokacin da ya karbi mulki, bashin da ake bin Najeriya Naira Tiriliyan 12 ne amma yanzu ya kai Naira Tiriliyan 32 kuma yana karuwa; sannan kuma hauhawar farashi tana kaso 9% a lokacin PDP amma yanzu ta haura kaso 15%; haka kuma rashin aikin yi yana kaso 8.9% amma yanzu ya kai kaso 33%; sannan naira da ake canza ta ga dala daya a naira 197 lokacin PDP yanzu ta haura naira 500; haka kuma man fetur da ake siyar shi naira 87 a shekarar 2015 yanzu kuma naira 165 a karkashin APC.

KU KARANTA: Buhari Ya Ki Bayyana Wanda Yake So Ya Gaje Shi Saboda Kariya

Jam’iyyar ta kara da cewa, “Shugaba Buhari kamata yai yai amfani da damar da gidan Talabijin na Channels ya ba shi, ya nuna damuwarsa, ya kuma nemi afuwar ‘yan Najeriya game da gazawarsa da kuma abin kunyar da gwamnatin APC ta jawo, maimakon kokarin boye matsalolin APC ta amfani da rashin gaskiya da sambatu kan magaji.

“Tunanin Shugaban Kasa kamar yanda ya bayyana a hirarsa da Channels TV ya tabbatar da tsoron ‘yan Najeriya na cewa APC ba ta yarda da tsarin demokaradiya ba, kuma ta yi shirin yin magudi a zaben 2023 karfi da yaji.

“Wannan ya nuna manufarsu ta rusa Kudirin Gyaran Dokar Zabe wanda zai bayar da damar aika sakamakon zabe ta na’ura, wanda hakan zai maganin shirin APC na yin magudi a zaben 2023.”

Jam’iyyar adawar ta gargadi Shugaban Kasa da jam’iyyar APC da su san cewa, ‘yan Najeriya sun amince da PDP ta jagorance su wajen kalubalantarsu a 2023.

Comments
Loading...