An bayyana Najeriya a matsayin kurar baya wajen anfani da bandaki a duniya, duba da alkaluman da ake da su, abin da ya sa ake da bukatar wayar da kai da kuma kara saka kudade a bangaren.
Kolawole Banwo, kwararren masanin muhalli kuma shugaban sashin wayar da kai na WaterAid Nigeria ne ya bayyana hakan a zantawarsa da jaridar TRIBUNE.
Ya bayyana cewa, masu ruwa da tsaki sun matsa kaimi wajen samar da wayewar kai da kuma sanya kudade musamman daga bangaren kamfanoni masu zaman kansu.
KARANTA: Zabtarewar Kasa A Malesiya Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 8
Kolawole ya ce, “Idan muka samu abin da muke sa ran samu daga Taron Duniya kan Bahaya na kwanannan, zamu iya samun nasara wajen samar da bayangida ga ‘yan Najeriya miliyan 113 da ba su da bayangida, sannan mu canza halayyar mutane miliyan 48 da suke yin bahaya a bainar jama’a.”
Ya bayyana tsananin burin da jama’a ke da shi a kansu a matsayin kalubalen da yake damunsu su da masu bayar da gudunmawa, abin da ya bayyana da rashin fahimtar yanda suke aiki.
Haka kuma ya bayyana bukatar gwamnati ta baiwa bangaren muhimmanci da sauran bangarori masu alaka domin samun nasarar da ‘yan Najeriya suke bukata.