For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Nigeria Miliyan 17 Za Su Gamu Da Yunwa

Daga: RFI Hausa

Kusan ‘yan Najeriya miliyan 17 ne aka yi hasashen za su fada cikin rikici ko matsanancin karancin abinci a shekara mai zuwa, a cewar wani rahoto.

Rahoton, wanda ake fitarwa duk bayan shekaru 2, an samar da shi ne karkashin jagorancin Ma’aikatar Aikin Gona ta kasar tare da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu.

A tsakanin watan Oktoba da Disamban wannan shekarar, fiye da ‘yan Najeriya miliyan 12 da dubu 100 a jihohi 21 na cikin yanayi na rikici, ko kuma matsanancin matsalar karancin abinci, kamar yadda rahoton da aka wallafa a Juma’ar da ta gabata ya bayyana.

Ya kara da cewa, ana hasashen wannan adadi zai karu zuwa miliyan 16 da dubu dari 800 a tsakanin watan Yuni da Agustan shekara mai kamawa.

Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, wannan sakamako da aka samu ta wajen hasashe, zai taimaka wa masu shata manufofi wajen gano yankuna da adadin al’ummomin da ke fuskantar hadarin karancin abinci da ma abinci mai gina jiki.

Comments
Loading...