Hukumar ‘Yan Sanda reshen jihar Jigawa ta kama wanda ake zargi da kasancewa babban dillalin kwaya, dan shekara 48 a karamar hukumar Hadejia.
Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar ‘yan sanda a jihar, ASP Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan a wani jawabi yau a Dutse.
Jami’in ya bayyana cewa, ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin a ranar 15 ga watan Nuwamba da misalin karfe 12:30 na rana.
Ya bayyana cewa, jami’an ‘yan sandan sun kama wanda ake zargin ne yayi wani samame a unguwar Gandun Sarki ta Hadejia.
Lawan Shiisu ya kara da cewa, an samu wanda ake zargin da kwalabe 43 da ake zargin na miyagun kwayoyi ne.
Ya kuma ce ‘yan sandan sun kuma cafke wadansu da ake zargin masu laifi ne su su shida a karamar hukumar Kiyawa.
Ya ce wadanda aka kama din, ‘yan shekaru tsakanin 35 zuwa 55 ne, an kuma kama su ne a guraren da ake zargin maboyar masu aikata laifuka ce a kauyen Balago a ranar 16 ga watan Nuwamba da misalin karfe 7 na dare.
Labari: Kabiru Zubairu