Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta ce, ta kashe mambobin kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB, a musayar wutar da suka yi a jiya Laraba.
Jaridar vanguard ta rawaito cewa an kuma kai samame sansanin ‘yan IPOB din, inda aka gano gurneti guda 13 da ake kyautata zaton kirar Rasha ne.
An kuma samu abin sanyawa mutane shokin na lantarki guda 210, da motocin alfarma guda 2 kirar Lexus 300, da babura masu dan karen gudu 5, da bindiga kirar pump action guda 2, da kananan bindigogi, ciki har da AK 47 da GPNG, da kakin soji kusan guda 30.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Ebonyi, SP Chris Anyanwu ya shaidawa manema labarai a birnin Abakaliki cewa, sun gano mutanen IPOB din a sansanonin da suka kafa a garuruwan Umuleje, Amaeze da Nkalaha a karamar hukumar Ishielu a jihar.