Daga: CHANNELS
‘Yan sanda dauke da makamai a motocin sintiri sun mamaye babban ofisihin Jam’iyyar All Progressives Congress, APC mai mulkin Najeriya a Abuja ranar Laraba.
Lokacin da sojojin suka isa sakatariyar, sun warwatsu sassan daban-daban na shiga da fita daga sakatariyar.
Wata majiya ta sanar da cewa, ‘yan sandan sun mamaye ginin sakatariyar ne bayan samun labarin cewa masu zanga-zanga na kokarin yin maci a harabar sakatariyar.
A lokacin da Channels take hada rahoton, jam’iyyar APC ba ta ce komai ba game da lamarin.
Ku kalli video kan labarin daga Channels TV.