‘Yan siyasa da manyan mutane 100 ne da suka hada da gwamnoni masu ci guda 14, tsofin gwamnoni 13 da tsofin shugabannin majalissar dattawa guda 3 sun hadu a Lagos domin kubutar da Najeriya da kuma samar da sasanto domin samar da sabuwar Najeriya.
Manyan mutanen, karkashin “The 2022 Committe’, sun ce dole ne a kubutar da Najeriya a sama mata zaman lafiya da hadin kai kafin a fitar da ‘yan takarar siyasa na shekarar 2023.
An baiyana hakanne a wata sanarwa da aka saki a yau Laraba, wadda Nduka Obaigbena daya daga cikin masu jaridar ThisDay, da kuma dan siyasa daga jihar Borno kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Asusun Tallafawa Ilimin Manyan Makarantu, Kashim Ibrahim Imam.
Sanarwar ta baiyana cewa, manyan mutanen sun yi ganawar ne a tsakanin 4 zuwa 6 ga watan Fabarairu na shekarar 2022.
Sanarwar ba ta kuma baiyana sunayen mutane 100n da suka hadu a Lagos din ba, sai dai kuma jaridar PUNCH ta gano cewa akwai manya daga jam’iyyar APC mai mulki da kuma jam’iyyar PDP da suka halarci zaman. Haka kuma mahalarta taron sun samo asali daga yankunan Arewa da Kudu.
Wasu daga cikin wadanda suka halarci zaman, wadanda wakilin PUNCH ya samu zarafin gani, sun hada da tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel; tsohon Shugaban Majalissar Dattawa kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim, wanda kuma dan takarar Shugaban Kasa ne a PDP; tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Bukola Saraki, kuma mai neman takarar Shugaban Kasa a PDP, tsohon Gwamnan Jihar Imo, Ikedi Ohakim; tsohon Gwamnan Jihar Cross Rivers, Donald Duke da kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore.
A sanarwar da aka saki ranar Laraba, Obaigbena da Ibrahim Imam sun ce manyan mutanen sun yi aiki a kananan kwamitoci guda uku na tsaro, tattalin arziki da batun sauyin mulki, inda suka baiyana cewa, mahalarta zaman sun fitar da cewa akwai bukatar yin aiki domin kawo daidaito a wannan matsanancin yanayin na sauyin mulki.
Sanarwar ta kuma baiyana cewa za a cigaba da ganawar har a samar da yanayin da za a samu ingantattun shugabannin da za su jagoranci Najeriya amatakai daban-daban a 2023.
Ta kuma baiyana cewa abun da Najeriya ke bukata a wannan lokacin shine dukkanin masu kishin kasa su fito su bayar da gudunmawa domin daidaituwar al’amura.