
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta ce siyan katin zabe da ake zargin wasu a Arewacin Najeriya da yi aikin kawai ne da ba zai anfanar da su da komai ba.
Mai Magana da Yawun INEC, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a tattaunawar da yai da gidan Talabijin na Channels a jiya Lahadi wadda kuma TASKAR YANCI ta bibiya.
A makon da ya gabata ne, Kungiyar Dattawan Arewa ta yi zargin cewa, wasu ‘yan siyasa na siyan katin zaben mutane a kan kudi naira 2,000 a yankin na Arewa.
“An sanya dubunnai ko ma miliyoyin ‘yan Arewa musamman mata, suna bayar da katin zabensu a kan abun da bai taka kara ya karya ba, a wasu lokutan a kan kudin da bai haura naira 2000 ba. Wani lokacin ana ce musu za a dawo musu da katinsu bayan an tantance su don a ba su kudin rage talauci. Ba a kuma dawo musu da katin,” in ji dattawan na Arewa.
Da yake magana a kan lamarin, mai magana da yawun INEC din ya ce, yin zabe da katin wani a zabe mai zuwa, wani abu ne da ba zai yiwu ba, inda ya kara da cewa, siyan katin kawai zai tauyewa masu zabe hakkinsu ne.
“Abubuwa biyu ne zasu yiwu a nan. Na farko shine ka kwacewa mutum katin zabensa ka hana shi ya yi zabe, zamu iya cewa kana aikin tauyewa masu zabe hakkinsu.
“Idan ka sayi katin zaben wani kuma mutumin bai samu damar zabe ba, hakan na nufin an rasa kuri’a daya, saboda haka kana rage yawan kuri’un wannan mazaba ne. Wannan a mataki na farko kenan.
“Abu na biyu shine, wasu ‘yan siyasar suna tsananin buri. Suna son samun damuna ne, suna tunanin akwai yiwuwar su iya yin magudi a BVAS wadda za a yi anfani da ita wajen tantance ‘yan takara.
“Na tabbatar da cewa aikin nasu ba zai tsinana komai ba. Duk wanda yake siyan PVCs yana aikin banza ne kawai. Abin da mai siyan PVC din nan zai iya yi kawai shine ya hana mamallakin katin yin zabe a ranar.
“Amma ka ce zaka zo a ranar zabe zuwa akwatu da katin zaben wani sannan kai kokarin wai zaka yi zabe, abu ne to da ba zai taba yiwuwa ba.
“BVAS ba zata taba daukar hoton yatsunka ba, ba zata taba daukar hoton fuskarka ba.”