For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Siyasar Da Zasu Rasa Mukamansu Saboda Sauya Sheka Zuwa APC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori Gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi tare da Mataimakinsa, Eric Igwe, saboda sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Alkalin Kotun, Alkali Inyang Ekwo, a hukuncin da ya yanke ranar Talata ya kuma kori ‘yan majalissu 15 na jihar wadanda suka hada da Kakakin Majalissar da wasu biyu da suka Umahi zuwa APC.

Alkali Ekwo ya kuma ce duk albashin da alawuns-alawuns da wadanda akai karar suka mora daga lokacin da suka sauya sheka zuwa wannan lokaci za a mayarwa gwamnatin jihar.

Da wannan abu da ya faru, gwamnonin jihohin Zamfara da Cross River, Bello Matawalle da Ben Ayade su ma zasu iya fuskantar irin wannan hukunci.

Ben Ayade

Ben Ayade

Tuni dai jam’iyyar PDP ta shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda take fatan kotun da kori Ben Ayade da mataimakinsa, Ivara Esu, saboda sauya sheka zuwa APC.

Ayade da Esu dai an zabe su ne a karkashin jam’iyyar PDP amma daga baya suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a ranar 20 ga watan Mayu na shekarar 2021.

A karar da lauyoyin jam’iyyar suka shigar karkashin jagorancin Babban Lauyan Najeriya, Emmanuel Ukala, jam’iyyar PDP ta nuna cewar mutanen jihar Cross River jam’iyyar PDP suka zaba wadda Ben Ayade ya yiwa takara, inda ta kara da cewa wannan dama ba zai yiwu ta koma ga jam’iyyar APC ko wata jam’iyya ba.

Bello Matawalle

Duk da kasancewar Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Gusau, Jihar Zamfara a watan Fabarairun da ya gabata ta kori karar da ke neman a kori Bello Matawalle da sauran wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a jihar, akwai wata karar a kansa a Kotun Koli.

Karar da jam’iyyar PDP ta shigar tana da goyon bayan shaida mai dauke da bayanai 26 wadda sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Umar Tsauri ya gabatar.

Jam’iyyar PDP a karar da Babban Lauyan Najeriya, Emmanuel Ukala yake karewa ta sako Shugaban Majalissar Dattawa, Ahmad Lawan, Kakakin Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila; Alkalin Alkalai na Jihar Zamfara; da kuma Kakakin Majalissar Dokokin Jihar Zamfara a matsayin wadanda ake zargi.

Karar ta kuma bukaci kariya kan yunkurin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau wanda bai bar jam’iyyar PDPn ba.

Bayan Ayade da Matawalle, su ma ‘yan majalissun da suka sauya sheka tare da su zuwa APC za su iya fuskantar kora daga kan muƙamansu idan har karar da akai ta yi nasara a kansu.

‘Yan Majalissu

Haka kuma dai, mukaman ‘yan majalissu biyu na Majalissar Dokokin Jihar Edo, Yekini Idaiye da Nosayaba Okunbor za su iya shiga halin tsaka mai wuya idan PDP ta shigar da su kara.

Idaiye da Okunbor da ke wakiltar Akoko-Edo 1 da Orhionmwon East sun sauya sheka zuwa APC a watan Fabarairun shekarar 2021.

A Majalissar Tarayya ma, ‘yan majalissu da dama na fuskantar wannan barazana ta kora daga kujerunsu saboda sauya sheka daga jami’iyyun da suka ci mulki zuwa wasu a duk kannin majalissun biyu na Dattawa da Wakilai.

A dai-dai watan Yunin 2021, yawan ‘yan Majalissar Dattawa da aka zaba a jam’iyyar PDP sun ragu daga 42 zuwa 38 a zaman majalissar na ranar Laraba 20 ga watan Yunin.

A wannan ranar, sanatocin PDP guda uku suka sanar da ficewa daga jam’iyyar ga Shugaban Majalissar wadda aka karanta a zauren majalissar.

Wadannan da suka sauya shekar sun hada da tsohon Mataimakin Marassa Rinjaye, Sanata Sahabi Ya’u (Zamfara ta Arewa), Sanata Lawali Hassan Anka (Zamfara ta Yamma) da Sanata Peter Nwaoboshi (Delta ta Arewa).

Kwana daya kafin hakan, Sanata Muhammad Hassan (Zamfara ta Tsakiya) ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC ta cikin wasikar ta ya baiwa majalissar.

A ranar 22 ga watan Fabrairu, Sanata mai wakiltar Taraba ta Kudu, Emmanuel Bwacha, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

(DAILY TRUST)

Comments
Loading...