For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mai Gari Da Wasu Mutum Hudu A Katsina

‘Yan ta’adda sun kashe Mai Gari, Alhaji Jafaru Rabi’u tare da yin garkuwa da wata wadda har yanzu ba a gano ta ba, a kauyen Daddara Liman dake karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina a daren Larabar jiya.

‘Yan ta’addar sun kuma kashe wasu mutane hudu a wani waje kusa da kauyen Daddara da ke karamar hukumar.

Mazauna kauyen sun baiyana cewa, ‘yan ta’addan sun bincike gidajen mutane tare da sace kayaiyaki da kuma kudade.

KU KARANTA: Hukumar Immigration Reshen Kano Ta Samu Sabon Kwantirola

Mai Magana da yawun Rundunar ‘Yansanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da faruwar al’amarin.

Ya ce, shugaban rundunar ‘yansandan yankin tare da jami’an sojoji wadanda suka samu labarin harin, sun yi musayen harbe-harbe da ‘yan ta’addar kafin ‘yan ta’addar su tsere.

Mai Magana da yawun ‘yansandan ya ce “’Yan bindigar, dauke da muggan makamai sun mamaye kauyen Daddara Liman da misalin karfe 11:30 na dare a ranar Laraba tare da yin harbe-harbe.

“DPO (na yankin) da jami’an sojoji sun kore su. Sun kashe mutane biyar da suka hada da digacin kauyen sannan kuma mutum daya ya bace.”

SP Isah ya kara da cewa, aiyukan sojoji da ke faruwa a jihohin Zamfara da Sokoto zasu iya zama sanadiyyar kwararowar ‘yan ta’addar zuwa jihar Katsina, inda ya kara da cewa jami’an tsaro a jihar suna yin duk mai yiwuwa domin ganin sun samu nasarar yakin tare da kawo karshen ‘yan ta’addar.

Comments
Loading...