Rahotanni na cewa, kimanin ‘yan bindiga 30 ne suka rasa rayukansu a wani rikici da ya barke tsakaninsu da mayakan kungiyar Ansaru a yankin Damari da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Jaridar Daily Trust aukuwar lamarin, inda suka ce, bangarorin biyu sun yi dauki-ba-dadin ne a makon jiya.
Wannan na zuwa ne makwanni uku da ‘yan ta’addan ke guje wa hare-haren sojoji a Zamfara tare da neman mafaka a kauyukan Birnin Gwari, inda suka kafa tutarsu.
RFI Hausa ta rawaito cewa; ‘yan ta’addar na Ansaru da suka yi kaka-gida a Birnin Gwari, sun hana ‘yan bindigar sace-sacen jama’a da kuma kaddamar da farmaki kan garuruwa.
Sai dai ‘yan bindigar sun yi watsi da gargadin na Ansaru, lamarin da ya haddasa rikici tsakanin bangarorin biyu kamar yadda rahotanni daga yankin suka tabbatar.