For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yan Ta’addar Kungiyar Boko Haram Ne Suka Kai Harin Gidan Yarin Kuje – Belgore

Babban Sakataren Ma’aikatar Lura da Harkokin Cikin Gida, Dr. Shuaibu Belgore ya ce ‘yan kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram ne suka kai harin da ya jawo balle gidan yarin Kuje.

Belgore ya bayyana cewa ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kai harin ne domin su kubutar da abokan ta’addancinsu da ake tsare da su a gidan yarin.

Belgore ya bayyana hakan ne a yau, lokacin da yake magana da ‘yan jarida a Abuja.

Ya kara da cewa, fursunoni sama da 600 ne suka tsere daga gidan yarin a lokacin da aka kai harin na jiya Talata da daddare.

Ya ce, a yanzu haka an samu nasarar kara kamo fursunoni 300, yayin da wasu sama da 300 ke waje har kawo yanzu.

Belogore ya kuma ce, a lokacin harin wani jami’in Nigeria Security and Civil Defence Corps ya rasa ransa.

Ya ce, “An sassamu hare-hare akan gidajen yarinmu, mafi yawa mun magance su, amma yau da kullum, akwai wadanda aka samu nasara a kan mu. A wannan karon sun zo a shirye da manya-manyan kayan fashewa.

“Shirinsu na farko na shiga gidan ya samu nasara, sannan sai suka kai hari wani bangaren na katangar gidan da abun fashewa babba, abun da ya jawo katangar ta ruguje.

“Jami’an da suke kasa a lokacin sun yi iya bakin kokarinsu wajen magance harin, amma yawan mutanen da suka zo da su na da yawa abun da ya fi karfin jami’an. Sun ci gaba da yakarsu amma dai a karshe an samu nasarar fasa gidan yarin. Daga baya an jami’an sun samu karin temako abun da ya sa suka dakile matsalar.

“A lokacin da suka zo sun kashe wani jami’in NSCDC a kokarinsu na samun nasarar aikinsu. Fursunoni 994 ne a nan.

“Mun gano cewa, ‘yan ta’addar kungiyar Boko Haram ne, kuma sun zo ne musamman domin ‘yan uwansu. Da yawansu sun dawo, wasu kuma an kamosu daga cikin daji inda suke boye. Yanzu haka mun dawo da kusan fursunoni 300 daga cikin kusan 600 da suka gudu daga gidan yarin.”

Comments
Loading...