For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yan Takarar Gwamna Na PDP 17 Sun Ziyarci Wike Har Gidansa

Akalla ‘yan takarar neman zama gwamna a jihohi 17 daga Jam’iyyar PDP ne suka gana da Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike a sirrance a daren ranar Talata.

An rawaito ‘yan takarar sun isa Birnin Port Harcourt wajen karfe 8 na dare, sannan nan take suka shiga ganawar da mai masaukin nasu.

Wata majiya daga Gidan Gwamnatin Jihar Rivers ta ce, akwai yiwuwar ‘yan takarar sun fito ne daga jihohin Katsina, Sokoto, Jigawa, Kaduna da kuma sauran wasu jihohin 13, kuma ganawar an yi ta ne a wani gidan Wike da ke Rumueprikon, a Karamar Hukumar Obio-Akpor.

Duk da ba a bayyana abun da aka tattauna a ganawar ba, akwai rade-radin cewa, ganawar na da alaka da zaben 2023 da kuma makomar jam’iyyar duba da rigingimun da take fama da su.

Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce, ‘yan takarar sun je ne domin su roki Wike wajen samun goyon bayansa ga takarar Atiku Abubakar da Dr. Ifeanyi Okowa da kuma mubaya’arsa ga Shugaban Jam’iyyar. Sanata Iyorchia Ayu.

Ganawar dai ta debi awanni biyu ne ana yinta.

Gwamnan Jihar Rivers din dai, tun bayan kammala zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa a Jamíyyar PDP wanda ya baiwa Atiku Abubakar nasara ne ya yi fushi da yanayin yanda jamíyyar tasu ke gudana.

Kuma tun bayan hakan ne dai manyan ‎’yan jam’iyyar ke ta yunkurin an magance matsalar domin samun cikakken goyon bayan gwamnan.

Comments
Loading...