Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya kuma tsohon Ministan Cikin Gida, Janaral Abdulrahman Dambazau ya ce, aiyukan yanta’adda da na haramtacciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafra suna zama barazana ga babban zaben shekarar 2023.
Dambazau, ya yi wannan magana ne lokacin da yake gabatar da jawabi mai taken: “Siyasar 2023: Tsaron Kasa da Daidaituwar Najeriya” a taron shekara na jaridar BLUEPRINT wanda aka gudanar a Abuja jiya Talata.
A jawabin nasa, Dambazau ya ce, “Shin matsalar rashin tsaro zata shafi zabukan 2023? Tabbas zata shafa, saboda har wannan lokacin wadansu al’ummun ba su da damar zama a muhallansu, kuma yanta’addar zasu iya ci gaba da kai hare-hare.
“Shugabannin INEC da ma’aikatan wucin gadi zasu zama ababan kaiwa hari duk da alkawarin gwamnati na kare su. Samu damar zuwa akwatinan zaben da ke guraren da ke kusa da iyaka zai yi wahala. Wannan kuma daya ne daga dalilai da dama da zasu sa dole a samar da tsaro.”