Tabbas duk al’ummar da ba zasu iya kare tarihinsu ba, tamkar rashin sanin kai ne da hangen nesa. Duk al’ummar da bata da tarihi tabbas lokaci zai shafe ta.
Irin wadannan hotunan kusan abubuwan da suka rage kenan a gineginen Turawan mulkin mallaka a garin Hadejia.

A yau ba a maganar ganuwar da ta kewaye garin na Hadejia, duk da kasancewar Kasar Hadejia da garin Hadejia sanannu ne a fadin Kasar Hausa, labarin tarihinsu da jarumtarsu ya kewaya duniya, har ya zama abubuwan da a ke bincike a kai a makarantu da guraren binciken neman ilimi da adana tarihi.
Manyan garuruwu tsarar Hadejia hatta ganuwar da ta kewaye garuruwan sun killace ta da kare ta domin tabbatar da tarihinsu, amma a nan ana hankoran mallakar filotai a wajen don arzuta kai. Mayar da guraren filin gina gida da zamewa kadara wannan gazawa ce ta ilimin tattalin arziki.
Hadejia ta yi kaurin suna a fadin duniya, fitatttun mutane a duniya su kan zo Hadejia don gani da ido, saboda tasirin da Hadejia tayi a tarihin duniya. Tarihin Bahaushe da Bayajidda ba ya cika sai ka sanya Hadejia da Biram ta Gabas.
Tarihin yaki da gwagwarmayar da aka yi da Hadejiyawa lokacin mamayar Turawan mulkin mallaka, wanda wannan gwagwarmayar da jajircewar Hadejiawan ta sanya Turawan Ingila suka sanya Hadejia a cikin tarihinsu na mulkin mallakar da suka yi a Afirka.
Mr. Philips, wanda a ke kira da Maitumbi, shine Baturen da ya jagoranci turawan Ingila mamayen Hadejia a 1903, wanda a wannan lokacin basu samu nasara ba, ya koma garin Katagum da ke Jihar Bauchi a yau, kafin da ga baya ya sake dawowa Hadejia a shekara ta 1904.
Kafin Turawan mulkin mallaka su sami galabar mamaye Hadejia, sai da aka yi gumurzu da yaki mai tarihi, a wannan yakin ne aka kashe Mr. Philips (Maitumbi), Turawan suka binne shi a nan kuma suka sanya alama a kabarin sa, wanda daga baya mutane suke rushe wannan kabarin na Maitumbi.
Madallah da kokarin da Dan Masanin Hadejia ya yi, President na ICAN Alhaji Tijjani Musa, wanda ya gyara kabarin da kuma killace shi. Wannan ba karamar gudunmawa bace don kare martabar Hadejia da kuma kare tarihin ta.
A lokacin mulkin mallaka, Hadejia ta kasance lardi wadda Larduna irin su Katagum wato Azare, Gumel, Kazaure duk suna karkashin lardin na Hadejia.
Yayin da kasashen da suka ci gaba da ma jahohi suke killacewa da adana kayayyakin tarihinsu, hatta alamomi da diddigen kayayyakin yan mulkin mallaka don ilmantar da mutane masu zuwa. Yau a cigaba ma na zamani abubuwa na tarihi sun zamanto hanyoyin bunkasa tattalin arziki ta hanyar yawan bude idanu, amma a irin wannan yanki namu rusa su ma muke yi don biyan karamar bukata ta kayuwan wasun mu.
Rusa kayan tarihi don mallakar fili ko foloti don gina gida a irin garin Hadejia mai isasshen fili da za a iya gina muhallai, ba karamin toshewar basira ba ce a ce irin wadannan gurare ake rusawa da mallakawa wasu tsirarun mutane.
Wadanna hotuna gine-gine ne tun na turawan Birtania na mulkin mallaka da offisoshinsu, amma abin takaici wadannan gine-gine da ma filayen wadannan gidajen an barsu suna rushewa.
Babban abin damuwar shine yanda gwamnati ta kekketa wuraren ta rabarwa wasu mutane daban domin gina gidaje, wanda a nan gaba tarihin wanna gurin zai shafe, ya zamanto babu komai. Tabbas wannan mataki da gwamnati ta dauka da duk masu hannu a ciki na rusa tarihin Hadejia, Najeriya da Ingila ba karamin kalubale bane a wannan zamanin da ma wanda zasu zo a gaba.
Ya kamata gwamnatin Jihar Jigawa da manyan masarautar Hadejia su duba wannan al’amari na yankawa da rarraba wadannan filaye. Ya kamata a killace su a inganta su domin masu zuwa yawan bode ido da ma masu neman tarihi. Amma wannan mataki tamkar nunawa duniya ne rashin sanin kai da kishin al’umarmu.
Daga: Ahmed A. Ilallah
alhajilallah@gmail.com