For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yanda Atiku Zai Magance Matsalar Tsaro – Okowa

Gwamnan Jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ifeanyi Okowa, ya ce dan takarar jam’iyyarsu na shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya gano cewa magance matsalar talauci da rashin aikin yi sune jigo wajen kawo karshen matsalar tsaro a kasa.

Da yake jawabi ga manema labarai a jiya Lahadi a Abuja, Okowa ya ce, akwai matukar talauci da rashin aikin yi a kasa, inda ya kara da cewa, “dole ne ka yi maganin wadan nan da farko; amma kafin haka ba za ka iya magance matsalar tsaro gaba daya ba.”

Okowa ya yi alkawarin cewa idan aka zabe su, gwamnatin Atiku Abubakar zata dage wajen samar da yanayi mai kyau ga ‘yan Najeriya domin su samu walwalar aiwatar da al’amuransu na yau da kullum ba tare da tsangwama ko tsoron hari ba.

“Zamu samar wa ‘yan Najeriya kwarin guiwa; wannan shine abun da zamu yi. Ya kamata a farfado da tattalin arziki. Mun yi maganar rarraba karfin gwamnati zuwa jihohi saboda duk lokacin da jihohi ke gasasseniya a tsakaninsu, kuma suna dagewa domin kyautatawa al’ummarsu, duk sassan kasar nan zai din ga samun ci gaba.

“Gwamnatin Tarayya za tai kokari wajen ci gaba da goyon bayan jihohi, amma fa suna da bukatar kudade daga cikin gida don su gina kan su; kananan hukumomi ma sun fi bukatar kudaden.

“Dole mu bayar da kulawa ta musamman ga bangaren ilimi; dole mu fara bai wa yawanmu muhimmanci da kuma samar da lafiya ga kowa,” in ji Okowa.

Comments
Loading...