Sashin Koyon Ilimin Aikin Jinya na Jami’ar Ahmadu Bello, ABU da ke Zaria, mutane uku kadai ya fitar masu matsayin digiri mafi daraja wato first class kuma dukkanninsu ‘yan Jihar Bauchi ne.
Wakilin THE NATION ya rawaito cewar, nasararsu na da alaka da jajircewa da kuma samun ginshiki mai kyau a karatunsu na baya.
A shekarar 2017, Usman Usman Muhammad ya kafa tarihi a Sashin Koyon Ilimin Aikin Jinya na ABU, Zaria, inda ya kammala karatun da digiri mai daraja ta daya a karon farko a tarihi, tun bayan fara sashin a shekarar 1997.
Usman ya samu wannan nasara ne bayan ya samu maki mai darajar 4.50 cikin 5.00.
Wannan nasarar ta karawa dalibai da dama kwarin guiwa, musamman wadanda suka fito daga jihar da Usman ya fito wato Jihar Bauchi.
Wani mai irin sunan na farko, Usman Usman Muhammad da kuma Abdullahi Muhammad Bello wadanda su ma ‘yan Jihar Bauchi ne, dukkanin su sun biyo bayan Usman na farko, inda Usman na biyu ya kammala karatunsa a wannan sashi da shaidar digiri mai daraja ta daya.
Usman na biyu ya kammala karatun ne da maki mai darajar 4.66 cikin 5.00, yayin da Abdullahi kuma ya kammala da maki mai darajar 4.55 cikin 5.00.
Mutum na farkon, wato Usman Usman Muhammad ya fito ne daga karamar hukumar Bauchi, yayin da matasa biyun da suka biyo bayansa suka fito daga karamar hukumar Kirfi duk a jihar Bauchi.
Wani abun mamaki shine, dukkanin su, su ukun, sun sami horo a matakin farko na koyon aikin jinya wato Basic Nursing Science a makaranta daya da ke Bauchi, School of Nursing, Bauchi kafin su dora a ABU su nemi karatun digiri.
A tattaunawar da akai da shi, Usman na biyun, ya baiyana cewa, ya san Usman na farko kuma yana gaba da shi School of Nursing, Bauchi, amma bai kammala karatun nasa na Bauchi ba ya shiga ABU ta hanyar JAMB.
Ya kara da cewa, lokacin da ya samu shiga ABU ta hanyar DE bayan ya kammala School of Nursing, Bauchi ya hadu da shi lokacin shi kuma yana shekararsa ta karshe.
Usman ya baiyana cewa, shima ya gwada shiga ABU, Zaria ta hanyar JAMB tun shekarar 2009 bayan ya gama karatun sikandire a Government College, Azare amma bai samu hakan ba, abin da ya sa ya fara da School of Nursing, Bauchi.
Matashin dan shekara 33 ya ce, kokarin da takwaransa yai na zama mutum na farko sashin na ABU da ya kammala karatunsa da digiri mafi daraja wato 1st class, shine ya kara masa kwarin guiwa ya dage shi ma.
“Lokacin da na gama, zango na biyu, takwara na ya kammala da first class. Sai na ji kwarin guiwa. Na cigaba da dagewa nai ta karatu, da jajircewa saboda nima na fita da first class kamar dai shi.”
Abdullahi Muhammad Bello shima yana gaba da Usman na biyun a School of Nursing, Bauchi, yana ma cikin wadanda suka wayar da kan su Usman akan karatu, kwatsam kuma sai suka zama ‘yan aji daya a ABU, Zaria bayan shi Abdullahi ya kammala karatun gaba da Basic Nursing wato Post Basic Nursing a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.