Babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake zamanta a Hadejia, jihar Jigawa, ta zartar da hukuncin daurin shekaru biyu a gidan ajiya da gyaran hali kan wani matashi bayan samunsa da laifin satar bustar ruwa ba tare da zabin biyan tara ba.
Matashin mai suna Aliyu Garba dan kimanin shekaru 20 a duniya, mazaunin unguwar Kwarin Madaki ne a cikin garin Hadejia, an tuhumeshi da laifin shiga gida da sata.
Dan sanda mai gabatar da kara a gaban kotun Insfector Hamisu Murtala, ya bayyanawa kotun cewa matashin ya tsallaka gidan wani mutum mai suna Alhaji Sale mazaunin unguwar Kwarin Madaki a Hadejia, inda ya sace bustar ruwa.
Hamisu Murtala, ya ce daga baya ne wanda ake zargin ya dawo neman wayarsa wanda ya ce ta fadi lokacin da ya shiga gidan, yayin da a nan ne aka damke shi zuwa ofishin ‘yan-sanda bayan ya bayyana cewa shi jami’in tsaro ne a yankin.
Da yake yanke hukuncin alkalin kotun Mai Shari’a Yusuf Ibrahim Harbo, ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bisa la’akari da sashi na 180 da kuma na 144 na Kundin Hukunce Hukuncen Shari’ar Musulunci na jihar Jigawa.
(Abdullahi Yawale)