For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yanda Wani Saurayi Dan Damfara Ya Yi Amfani Da Kudin Damfara Wajen Dawainiyar Binne Mahaifinsa

An yankewa wani saurayi dan shekara 21, Ifeanyi Egbuwu, hukuncin zaman gidan yari na shekara daya saboda kama shi da yin damfara ta yanar gizo.

Jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, sun kama Egbuwu ne a ranar 2 ga watan Agusta, 2022 lokacin da suka kai samame kan wadanda ake zargi da damfara ta yanar gizo a 42, Ola Williams Street, Kay Farm Estate, Iju, Jihar Lagos.

Egbuwu, wanda ya ce ya kammala karatun sikandire kwananan a Oregun Senior High School, ya bayar da dama ga EFCC ta shiga email nasa, omohhenry79@gmail, inda aka same shi da aiyukan da suka shafi damfara.

Ya kuma bayyanawa EFCC din cewa, ya more naira 500,000 daga aiyukan damfarar da yai, inda ya ce, ya sayi iPhone X daga cikin kudin sannan yai amfani da wasu wajen hidimar binne mahaifinsa da ya rasu.

Bayan samunsa da laifin, alkalin kotun ya yanke wa Egbuwu hukuncin zaman gidan yari na shekara guda ko kuma ya biya tarar naira 300,000 da kuma aikin temakon al’umma na awanni 100 a gidan yarin Kirikiri.

Alkalin ya kara da cewa, aiyukan temakon al’ummar da Egbuwu zai yi sun hada da yin aski tun da ya bayyana cewa ya iya sana’ar aski kafin ya shiga harkar damfarar.

Comments
Loading...