For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yanda Za A Magance Matsalar Zagwanyewar Likitoci A Najeriya

Shugaban Kungiyar Likitoci ta Najeriya, NMA, na Jihar Oyo, Wale Lasisi ya yi kira ga gwamnati da ta baiwa likitoci kudade domin magance zagwanyewarsu.

Lasisi ya yi wannan kiran ne a Ibadan a jiya Talata, a lokacin bude Satin Litikitoci na Shekarar 2022 mai taken: “Tsarin Samar da Lafiya a Najeriya da Sauyin Mulki a Shekarar 2023: Lokacin Samar da Sauyi.”

Ya bayyana cewa, ana da matsalar zagwanyewar likitoci a Najeriya tun shekarar 1960, yayin da mutane da dama ke barin Najeriya a kowacce rana.

Ya kara da cewa, “A shekarun baya, tsarin shine mutane suna fita kasashen waje ne domin su samo horo sannan su dawo gida su yi aiki.

“Amma da abubuwa ke lalacewa, wadanda suka san waje suna komawa, sannan wadanda suka yi karatun ma a wajen suma suna komawa can saboda ingancin aikin da ake da shi a can da suka gani.

“Birtaniya na kokarin bunkasa aikin samar da lafiyar ‘yan kasartan ta yanda zasu samu ingantacciyar kulawar lafiya, saboda haka sai suke zuwa kananan kasashe a Afirka, ciki har da Najeriya dominsu debi ma’aika.”

“Abu na gaggawa da gwamnati zata yi kan matsalar shine ta kara inganta walwalar ma’aikatan da ake da su domin su zauna,” in ji Lasisi.

Comments
Loading...