Domin rage radadin talauci da tallafawa domin fara sana’a ko kasuwanci, Gwamnatin Tarayya tana bayar da tallafin bashi ga masu sha’awar karba.
Wannan tallafin bashi babu kudin ruwa a cikinsa, kuma wadanda suka karba za su biya ne cikin a kalla shekaru 3 daga lokacin da suka karbi tallafin.
An kasa tsarin tallafin bashin ne gida 3, akwai bangaren HOUSEHOLD, SME da kuma AGSMEIS, to amma a wannan rubutun zamu yi bayani ne kan HOUSEHOLD, sai kuma a rubutu na gaba za mu dora da sauran.
An ware bangaren HOUSEHOLD ne domin masu son tanadar kayayyakin amfanin gida ko fara sana’a ko kasuwanci.
Wannan bangaren ba ya bukatar wasu bayanai masu wahala sosai, abin da ake bukata ga me sha’awar cike neman tallafin a wannan bangaren shine, BVN da sauran bayanai kanana.
Za a nemi tallafin kudin da bai haura naira 500,000 ba ne a wannan bangare, haka kuma za a rubuta sunaye da kudaden abubuwan da ake nufin mallaka domin gida ko sana’a ko kasuwanci.
Akwai bukatar yin taka-tsantsan wajen cike kudaden abubuwan da ake bukata domin kar su haura naira 500,000, domin mutane da yawa suna rasa tallafin saboda haura ka’idar da aka shimfida, amma ana iya neman kasa da haka.
Bayan kammala cikewa, wanda ya cike ya kula da lambar wayarsa sosai domin karbar sako kan abun da zai yi a gaba domin karbar kudin tallafin.
Ga masu sha’awar neman wannan tallafi bangaren HOUSEHOLD za su iya danna kasa👇
NEMAN TALLAFIN NIRSAL BANGAREN HOUSEHOLD
Abdurrahman Zubairu
Raudha Media Services, Birnin Kudu
09064114593