For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Yanda Ƴanbindiga Suka Ciyar Da Karnukansu Naman Direban Ƴan’uwana – Wani Malami A Sokoto

Sheikh Bashar Danfili, wani sannanen malami a Jihar Sokoto, ya nemi taimakon kudi daga jama’a bayan ƴan bindiga sun sace ƴan’uwansa guda shida a hanyarsu zuwa wani ƙauye a jihar.

Ya bayyana hakan ne a cikin wani gajeren bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa waɗanda aka sace sun hada da wani mutum, mahaifiyarsa, kishiyar mahaifiyarsa, matansa guda biyu, da kuma kanwarsa.

Sheikh Danfili ya ce ‘yan bindigar sun nemi makudan kudade da ba su da damar tarawa, kuma wa’adin biyan kudin yana kara ƙuratowa.

Malamin ya bayyana cewa, “Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan’uwana na kusa, kuma bana so na bayyana sunayensu.

Suna kan hanyarsu zuwa wani ƙauye lokacin da aka kai musu hari aka sace su. Direbansu an kashe shi nan take, kuma ƴan bindigar sun ciyar da karnukansu da naman direban.

Sai dai sauran mutanen suna tsare har yanzu, ciki har da miji, mahaifiyarsa, kishiyar mahaifiyarsa, matansa biyu da kanwarsa.

“Ƴan bindigar sun nemi makudan kudade da suka kai miliyoyin Nairori, kuma ba za mu iya tara wannan kudin ba. Ni malami ne, ba ni da komai sai karatu da koyarwa da nake yi da littattafan da kuke gani a bayana.

Sun ba mu wa’adin da za a biya kudin ko kuma su kashe su. Na san zasu iya yin haka ganin abin da ya faru da wani shugaban gargajiya a jihar da suka kashe. Don haka, ina rokon taimakon jama’a domin mu samu damar biyan kudin fansa da ceto su.”

Comments
Loading...