Daga: Abdullahi Yawale
Rundunar yan sanda a jihar bauchi ta kama wani matashi da ake zargi da kwacen babur.
Matashin mai suna Abdullahi Bakoji ya ce yana amfani da guduma wajen kwacen babur Inda yake boye ta a cikin wandonsa.
Sai dai matashin yace yana nadamar aikata wannan aika aika, don haka ya nemi ayi masa afuwa.
Kakakin rundunar yan sanda a jihar ta Bauchi DSP Ahmed Muhammad Wakil shi ne ya jagoranci gabatar da wanda ake zargin a gaban manema labarai.
DSP Wakil ya ce za su gurfanar da wanda ake tuhumar a gaban kotu da zarar an kammala bincike.