For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Yansanda A Zamfara Sun Kama Masu Ci Da Siyar Da Naman Mutane

‘Yansanda a jihar Zamfara sun kama mutane 8 da ake zargi da aikata babban laifi da yake jawo kisa, ta’ammali da sassan jikin mutane, tsafi, sata da kuma lalata wayar wutar lantarki.

Bayanan yanda aka kama wadanda ake zargin ya zo ne a cikin sanarwar da Kwamishinan ‘Yansanda na jihar Zamfara, CP Ayuba Elkanah ya fitar.

Kwamishinan ya ce, da misalin tsakar ranar Lahadi, 12 ga watan Disamban da ya gabata ne wani da ake kira da Aliyu Yakubu Aliyu ya sanar da batan dansa dan shekara 9 ga ofishin ‘yansanda na Gusau.

Lokacin da ‘yansanda suka karbi rahoton, masu gudanar da bincike suka shiga aikinsu, suka fara gudanar da zuzzurfan bincike kan lamarin.

Bayan haka ne, a ranar wata Talata, 28 ga watan Disamban, ‘yansanda suka sami rahoton asiri da ya shafi abatan yaron, kuma a wannan ranar ne aka sami wata gawa a wani kango a yankin Barakallahu da ke Gusau, an daure hannaye da kafafun gawar da tsumma a tare, an kuma rufe kanta da leda.

Masu binciken sun isa wajen, inda suka samu cewar, gawar ta yaron da aka sanar ya bata ce, daga bisani aka kai gawar asibiti domin bincike.

KU KARANTA: Wani Mutum Ya Kashe ‘Ya’yansa 3 Ya Boye Gawarsu A Firji

A cigaba da bincike kan lamarin, ‘yansanda a ranar Talata 4 ga watan Janairun da muke ciki, sukai amfani da rahoton sirrin da suka samu, suka kama wadansu mutane hudu da ake zargi da kisan.

Wadanda aka kama din sun hada da Aminu Baba dan shekara 57, Abdulshakur Muhammad dan shekara 20, Abdullahi Buba dan shekara 17 da kuma Ahmad Tukur dan shekara 14.

Abubuwan da aka samu a wajen wadanda ake zargin sun hada da “hanji, makogwaro, azzakari da kuma idanuwa guda biyu”.

A lokacin da ake tuhumarsu, daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Abdulshakur Muhd ya amsa laifin, inda ya bayyana cewa, wannan shine karo na uku da Aminu Baba yake sa shi nemo sassan jikin mutum a kan kudi N500,000.

Abdulshakur ya cigaba da cewa, shi da sauran mutane biyun da ake zargi, sun yaudari yaron da suka kashe, inda suka kai shi kangon suka kashe shi, suka kuma cire sassan jikinsa da suka hada da: hanji, makogwaro, azzakari da kuma idanuwa guda biyu.

Ya kara da cewa, sun dauki sassan jikin yaron inda suka kai su wajen Aminu Baba wanda ya biyasu kudi naira dubu dari biyar (N500,000) kamar yanda sukai alkawari a farko.

Kwamishinan ‘yansandan ya bayyana cewa, mutumin da ake kira da Aminu Baba wanda mahaifi ne ga yara 9, ya amsa laifinsa, kuma bayanansa suna temakawa ‘yansanda masu bincike wajen kara gano abokan aikinsa.

Aminu Baba ya bayyana cewa, lokuta da dama yana cin sassan jikin mutunen ne sannan kuma ya siyar da sauran.

Kwamishinan ‘Yansanda CP Elkanah ya yi kira ga al’umma da su marawa jami’an tsaro baya wajen magance aikata miyagun laifuka a jihar ta Zamfara, sannan su cigaba da addu’ar samun zaman lafiya da lumana a Zamfara da sauran sassan Najeriya.

Comments
Loading...